Hausa translation of the meaning Page No 179

Quran in Hausa Language - Page no 179 179

Suratul Al-Anfal from 17 to 25


17. To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. ( 1 ) Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
18. Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
19. Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!
20. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.
21. Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: « Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji. »
22. Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.
23. Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa,dã sun jũya , alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
24. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
25. Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
( 1 ) Kisan da aka yi musu, Allahne Ya kashe su, haka Annabi ya ɗẽbi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jẽfa wa kãfirai, tsakuwar ta shiga cikin idãnun kõwane ɗaya daga cikinsu. To, wannan jĩfar daga Allah take. Sabõda haka duk ganĩmar dai ta Allah ce da ManzonSa, sai yadda Ya so, zã a raba ta.