Hausa translation of the meaning Page No 177

Quran in Hausa Language - Page no 177 177

Suratul Al-Anfal from 1 to 8


Sũratul Anfãl
Tanã karantar da cẽwa taimakon Allah, shĩ ne nasara ga mãsu taƙawa, bã ƙarfinsu ba, da kuma shiryarwa ga dõkõkin yãƙi da abin da ya rãtayu da yãƙi dõmin ɗaukakakalmar Allah.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Suna tambayar ka ( 1 ) ga ganĩma. ka ce: « Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai. »
2. Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
3. Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa. ( 2 )
4. Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.
5. Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.
6. Sunã jãyayya da kai a cikin ( sha'anin ) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.
7. Kuma a lõkacin ( 3 ) da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;
8. Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.
( 1 ) Yã fãra Sũrar da tambayar Annabi cẽwa. Wãnne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin. Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau, Sa'annan ya yi jawãbi da cẽwa: « Ka ce ganimar ta Allah ce daManzonSa, » sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkyia. AllahYa fi sani.
( 2 ) Watau sunã yin ibãda ta jikida ta dũkiya wãjiba da nãfila.
( 3 ) Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito dagaMakka da ãyari zuwa Shãm, watau « Syria » , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya yaƙin kuraishãwa shĩ. ne wajen da yake da ƙaya.Musulmi a tsakiya Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra .Ya nẽmikuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye.