Hausa translation of the meaning Page No 180

Quran in Hausa Language - Page no 180 180

Suratul Al-Anfal from 26 to 33


26. Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku ( a wurin natsuwa, Maɗina ) , kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.
27. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.
28. Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma.
29. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba ( da tsõro ) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.
30. Kuma a lõkacin da waɗanda ( 1 ) suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
31. Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: « Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko. »
32. A lõkacin da suka ce: « Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi. »
33. Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, ( 2 ) kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.
( 1 ) Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina.
( 2 ) Rãyuwar Annabi a cikin mutãne aminci ne daga azãba, haka kuma yin istigfãri aminci ne wanda ke son wadãta da aminci daga Allah, sai ya lazimci istigfãri da bin sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.