Hausa translation of the meaning Page No 184

Quran in Hausa Language - Page no 184 184

Suratul Al-Anfal from 53 to 61


53. « Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ,Masani. »
54. Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci.
55. Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba.
56. Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa.
57. To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre ( 1 ) waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.
58. Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara.
59. Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba.
60. Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, ( 2 ) kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku.
61. Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.
( 1 ) Wãtau a kashe waɗandaaka kãma dõmin saura su gani su ji tsõro.
( 2 ) Tattali daga wani ƙarfi, ya haɗa dukkan abin da zai yiwu a yi yãƙin abõkin gãba da shi. A yanzu daga bindiga da abin da yake sama da ita,shi ne zã a yi tattali.