Hausa translation of the meaning Page No 188

Quran in Hausa Language - Page no 188 188

Suratul Al-Taubah from 7 to 13


7. Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.
8. Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.
9. Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana.
10. Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi.
11. Sa'an nan idan sun tũba ( 1 ) kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki- daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
12. Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.
13. Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance mũminai!
( 1 ) Rukunõnin Musulunci biyar ne: Kalmar shahãda da salla da azumi da zakka da hajji ga Ɗãkin Allah. Ana yãƙar mutum sabõda barin uku daga cikinsu, watau kalmar shahãda da salla da zakka kawai. Kuma uku sunã lazimtar mawãdaci da matalauci. Su ne kalmar shahãda da salla da azumi kawai. Amma zakka da hajji sai ga mai hãlin yi da wadãta.