Hausa translation of the meaning Page No 187

Quran in Hausa Language - Page no 187 187

Suratul Al-Taubah from 1 to 6


Sũratut Tauba
Tanã bãyani ga hukuncin yanke wa kãfirai na kõwane irin kãfirci, da irin alãƙa wadda take iya ragẽwa a tsakanin Musulmi da kãfiri da bayãnin siffõfin kãfirai.
1. Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu shirki ( 1 )
2. Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu, ( 2 ) kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.
3. Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa ( haka ) . To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi.
4. Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.
5. Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara,Mai jin ƙai.
6. Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba.
( 1 ) Kãfirai iri uku ne: mãsu addinin al'ãda kamar Lãrabãwa shũ ne mãsu shirki, sa'an nanmãsu bin Littãfi shãfaffe watau Yahudu da Nasãra sa'an nan da munãfukan wannan al'umma. Ya fãra da mãsu shirki da bayãnin irin ayubansu, sa'an nan ya yi bayãnin sauran kamar haka.
( 2 ) Bãyan yanke sulhu, Allah Yabai wa kãfirai watã huɗu na amãna, dõmin su ƙãre harkõkinsu da wasu ma'amalõli da suka ƙulla tãre da Musulmi, sa'an nan yãƙi ya tãshi. Anã nufin mãsu addinin al'ãda na shirki a nan.