Hausa translation of the meaning Page No 19

Quran in Hausa Language - Page no 19 19

Suratul Al-Baqarah from 120 to 126


120. Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: « Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. » Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki.
121. Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi ( Alƙur'ãni ) . Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
122. Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku ( 1 ) tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.
123. Ku ji tsõron wani yini, ( a cikinsa ) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba.
124. Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: « Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne. » Ya ce: « Kuma daga zũriyata. » Ya ce: « AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba. »
125. Kuma a lõkacin da Muka sanya Ɗãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: « Ku tsarkake ƊãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada. »
126. Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: « Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira. » Allah Ya ce: « Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana. »
( 1 ) Kira na ƙarshe zuwa ga Yahũdu dõmin shiga Musulunci. An biyar da gargaɗi gare su da tunãtar da su cẽwa wannan addinin fa, shi ne addinin kãkansu Ibrãhim, dõmin kada su fanɗare daga addinin ubanninsu na ƙwarai. Kuma sunã da lãbãrin ginin Ɗakin Ka'aba da addu'ar da lbrahim ya yi alõkacin, wadda ta ƙunshi zuwan annabi daga cikin zuriyar Isama'ila a Makka, watau Fãrãna.