Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 18
Suratul Al-Baqarah from 113 to 119
113. Kuma Yahũdãwa suka ce: « Nasãra ba su zamana a kan kõme ba, » kuma Nasãra suka ce: « Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba, » ( 1 ) alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Ƙiyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.
114. Kuma wãne ne mafi zãlunci ( 2 ) daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma.
115. Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi.
116. Kuma suka ce: « Allah Yã riƙi ( 3 ) ɗã. » Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.
117. Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: « Kasance. » Sai ya yi ta kasancewa.
118. Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: « Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana? » ( 4 ) Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.
119. Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta.
( 1 ) Mai gaskiya idan marasa gaskiya sun tãru sunã faɗa da shi, to, rashin jituwar tsakãninsu zai sanya Allah Ya kange shi daga sharrinsu, sũ duka, kamar husumar da ke tsakãnin Yahũdu da Nasãra da kuma tsakãnin sũ mushirikai, su duka mãsu yãƙi da Musulmi ne kuma mãsu sãɓã wa jũnã ne wajen aƙidõjinsu.
( 2 ) Misãlin sãɓãni tsakãninsu; Nasãra suka taimaki Bukht Nassara ga ɓata masallacin BaitilMaƙdis da jẽfa mũshe da shãra a ciki, dõmin ƙin Yahũdu. Wannan ƙiyayya tã bayyana har a cikin takardar alƙawari a tsakãnin Nasãra da Halifa Umar bn Khattãb suka ce kada ya bar Yahũdu su shiga Baitil Maƙdis. Sabõda haka idanwasu sun hana ku isa ga masallacinku kõ kuma suka jũyarda ku daga Alƙibla, to, kada ku ji kõme, sun yi irin aikin danginsu. Gabas da yamma na Allah ɗai ne, duk inda aka jũyar da ku, to, a can yardar Allah take. A lõkacin Musulmi na dũbin Baitil Maƙdis ga salla a bãyan Hijira daga Makka, bã su son haka.
( 3 ) Misãli na biyu Yahũdu na cẽwa Uzairu ɗãan Allah, kuma Nasãra sunã cẽwa Ĩsa ɗan Allah, Lãrabãwa na cẽwa Malã'iku 'ya'yan Allah. Wannan zai hana su jituwa har adãwarsu ga Musulmi ta yi tãsĩri.
( 4 ) Misãli ne ga irin rikicin mushirikai ga addini kuma da yadda suka yi kamã da Yahũdu, waɗanda suka ce wa Mũsã: « Ka nũna mana Allah bayyane. »