Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 20
Suratul Al-Baqarah from 127 to 134
127. Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga Ɗãkin, da Ismã'ĩla ( suna cẽwa: ) « Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani. »
128. « Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama ( al'amari ) gare Ka, kuma daga zuriyarmu ( Ka sanya ) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama. »
129. « Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo ( 1 ) daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin ( 2 ) da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima. »
130. Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai.
131. A lõkacin da Ubangijinsa Ya ce masa: « Ka miƙa wuya, » ya ce: « Nã miƙa wuya ga Ubangijin tãlikai. »
132. Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu ( ya yi wasiyya,suka ce: ) « Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi. »
133. Ko kun ( 3 ) kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: « Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna? » Suka ce: « Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne. »
134. Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa.
( 1 ) Addu'ar an karɓa, ta aiko Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
( 2 ) Littãfin- ya bayyana cẽwa Alƙur'ãni ne, dõmin bãbu wani sai shi. Hikima kuwa ita ce shari'ar da ke a cikinsa. Zai tsarkake su daga dauɗar shirki idan sun bĩ shi.
( 3 ) Lamĩrin Yahũdãwan Madĩna ne na zãmanin Annabi, waɗanda ake kira zuwa ga Musulunci anã tunãtar da su abinda kakansu lsrã'ĩla ya yi wasiyya da shi zuwa ga ɗiyansa, kãfin ya mutu; watau wannan aƙĩda da ake kiran suyanzu zuwa gare ta.