Surah At-Taubah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 191
Suratul Al-Taubah from 27 to 31
27. Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancana kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai rahama.
28. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci ( 1 ) to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.
29. Ku yãƙi waɗanda ( 2 ) bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
30. Kuma Yahũdãwa suka ce: « Uzairu ɗan Allah ne. » Kuma Nasãra suka ce: « Masĩhu ɗan Allah ne. » Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?
31. Sun riƙi mãlamansu ( 3 ) ( Yahũdu ) da ruhubãnãwansu ( Nasãra ) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama ( haka ) . Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi.
( 1 ) Idan kun ji tsõron talauci sabõda hanã mushirikai zuwa hajji sabõda fataucinku da su zai rage, to, bãbu kõme, arziki ga Allah yake, Yanã bãyar da shi ga wanda Yake so.
( 2 ) Bãyan gama hukuncin alãƙarMusulmi da kãfiran farko, watau mãsu shirkin, Lãrabãwa, sai kuma ya fãra bayãnin alãƙar Musulmi kãfirai na biyu; watau Yahũdu da Nasãra.
( 3 ) Hibru shi ne mãlamin Yahũdãwa, Ruhubãni mai ibãda wanda ya yanke jin dãɗin dũniya daga kansa sabõda ibãda, daga cikin Nasãra, mabiyan,gẽfen biyu sun riƙi shũgabanninsu ubanningiji sunã bauta musu, watau sunã yanka musu dõkoki waɗanda ba naAllah ba, sũ kuma sunã bin su a kan haka. Bautar da suke yi wa Uzairu kõ Masĩhu, Ĩsaɗan Maryama dõmin sun ce sũ ɗiyan Allah ne, watau sun zama juz'inSa ke nan. Tsarki ya tabbata ga Allah daga waɗannan siffõfiduka.