Hausa translation of the meaning Page No 192

Quran in Hausa Language - Page no 192 192

Suratul Al-Taubah from 32 to 36


32. Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.
33. Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.
34. Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr ( 1 ) da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
35. A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, ( a ce musu ) : « Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska. »
36. Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin ( 2 ) Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
( 1 ) Jam'in Hibru watan malamin Yahũdãwa.
( 2 ) Kõ dã, a cikin waɗannan watanni akwai mãsu alfarma, kõ da yake sũ kãfirai ba sa kiyaye alfarmarsu ba, sun shigar da wani wãyonsu a ciki wanda suke cẽwa Nasĩ'u ( watau jinkiri ) ; Idan sunã son su yi yãƙi a cikin ɗayan watannin, sai su halattar da shi, sa'an nan su haramta wani watã a matsayinsa, su ƙãra kãfirci a kan kafircinsu, da yin haka. Sabõda haka Allah Ya halattar da yãƙi a cikin kõwanne watã dõmin kada a mãmayi Musulmi. Kuma yin jihãdi Yanã cikin ayyukan ibãda wadda Allah Yake riɓanya lãdarta a cikin watannin, mãsu alfarma.