Hausa translation of the meaning Page No 193

Quran in Hausa Language - Page no 193 193

Suratul Al-Taubah from 37 to 40


37. Abin sani kawai, « Jinkirtãwa » ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.
38. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, « Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah, » sai ku yi nauyi ( 1 ) zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.
39. Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku ( a maimakonku ) . Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
40. Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: « Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu. » Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
( 1 ) Nauyi zuwa ga ƙasa, watau ku ƙãsa tãshi tsaye balle mã ku fita zuwa yãƙin da aka neme ku da shi ( sabõda shi ) . fita da yãƙi a nan, anã nufin yãƙin Tabũka a cikin lõkacin bazara, kuma bãbu abinci dõmin Allah Ya jarrabi Musulmi, Ya fitar da mũminai da kuma munãfukai, dõmin a san yadda zã a yi ma'ãmala da su. Haka kuma a kõwane lõkaci Allah Yakan sanya wani abin jarraba na wahala a cikin Musulmi dõmin Ya bambanta mũminai daga munãfukai.