Hausa translation of the meaning Page No 194

Quran in Hausa Language - Page no 194 194

Suratul Al-Taubah from 41 to 47


41. Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
42. Dã yã kasance ( 1 ) wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa.Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, « Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku. » Sunã halakar da kansu ( da rantsuwar ƙarya ) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'
43. Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.
44. Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.
45. Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.
46. Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu ( 2 ) zama.
47. Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,
( 1 ) Ya Shiga bayãnin siffõfin munãfukai waɗanda suka ƙi fita da waɗanda suk fitazuwa Tabũka, da waɗanda suka nẽmi wani uzuri, a cikin siffõfi dabam- dabam da zã a iya gane munãfukai da sua cikin kõwane zãmani na rãyuwar Musulmi a dũniya.
( 2 ) Watau mãtã da yãra da gajiyayyu.