Hausa translation of the meaning Page No 198

Quran in Hausa Language - Page no 198 198

Suratul Al-Taubah from 69 to 72


69. Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
70. Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta.
71. Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri ( 1 ) kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
72. Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
( 1 ) Abin da aka sani ga sharĩ'a shĩ ne alhẽri, kuma abin da da ba a sani ba ga sharĩ'a shĩ ne abin ƙi wanda bã a so.