Hausa translation of the meaning Page No 199

Quran in Hausa Language - Page no 199 199

Suratul Al-Taubah from 73 to 79


73. Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar!
74. Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su,kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.
75. Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, « Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai. »
76. To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,
77. Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.
78. Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake?
79. Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.