Hausa translation of the meaning Page No 197

Quran in Hausa Language - Page no 197 197

Suratul Al-Taubah from 62 to 68


62. Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai.
63. Shin, ba su sani ba cẽwa « Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba! »
64. Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu,wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: « Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro. »
65. Kuma lalle ne, idan ka tambaye ( 1 ) , su haƙĩƙa, sunã cẽwa, « Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: » Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili? « »
66. « Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi. »
67. Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu ( 2 ) daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri.Kuma sunã damƙẽwar hannayensu.Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.
68. Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya.
( 1 ) Ana a cikin tafiya zuwa Tabũka sai wasu mutãne daga cikin munãfukai suka ce wa junansu, « Wannan Yana zaton ya ci gidajen Rumawa da Biranensu? faufau. » Sai Allah Ya sanar da AnnabinSa ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) abin da suka faɗa. Sai ya ce: « Ku zo mani da waɗanean mutãne. » Da suka je masa ya ce musu 'Kun ce kaza da kaza.' Sai suka yi rantsuwa da cẽwa: ba mu kasance ba sai muna hĩra muna wãsã.
( 2 ) sũ duka daidai suke ga hãlinsu na sharri. Damƙe hannu shi ne rõwa.