Hausa translation of the meaning Page No 202

Quran in Hausa Language - Page no 202 202

Suratul Al-Taubah from 94 to 99


94. Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: « Kada ku kãwo wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa ( zai gani ) . Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
95. Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.
96. Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai.
97. Ƙauyãwã ne mafi tsananin ( 1 ) kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
98. Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda ( 2 ) suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.
99. Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma sunã riƙon abin da suke ciyarwa ( tamkar ) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita ( ciyarwar nan ) ibãdar nẽman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
( 1 ) Ƙauyãwã ne mafi tsananin kãfirci dõmin nĩsansu daga sanin hãlãyen girmamãwã da na zamantakẽwa, sa'an nan da nĩsansu daga Annabi har su saurari abin da ya zo da shi.
( 2 ) Ƙauyãwã kashi biyu ne: Akwai wãwãye munãfukai mãsu ganin addĩni yã ɗõra musu nauyin biyan zakkã da sauran ayyukan alhẽri, sunã ɗaukar sa kamar tãra da biyan kakkarai. Kuma akwai ƙauyãwa mãsu hankali sun sani Annabi manzo ne daga Allah, sunã ɗaukar abin da addĩni ya azã musu duka ibãda ne, sunã fãtar kusanta da shi zuwa ga Allah, Ubangjinsu. To su mutãnen ƙwarai ne, zã su shigã Aljanna.