Hausa translation of the meaning Page No 201

Quran in Hausa Language - Page no 201 201

Suratul Al-Taubah from 87 to 93


87. Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama ( a cikin gidãje ) . Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.
88. Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
89. Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma.
90. Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su.
91. Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ( 1 ) ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.
92. Kuma bãbu ( laifi ) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: « Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa, » suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba.
93. Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne.Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya ( gidãje ) , kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa.
( 1 ) Nasĩha ita ce su faɗi maganar ƙwarai; kyautatãwa itace a yi aiki dõmin Allah, ba dõmin nẽman dũniya ba.