Surah At-Taubah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 203
Suratul Al-Taubah from 100 to 106
100. Kuma mãsu tsẽrẽwa ( 1 ) na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; Ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.
101. Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, ( 2 ) haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.
102. Kuma da waɗansu, sun yi furuci ( 3 ) da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
103. Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.
104. Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyinSa, kuma Yanã karɓar sadakõkinsu, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai?
105. Kuma ka ce: « Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
106. Kuma da waɗansu waɗanda ( 4 ) aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu.Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
( 1 ) Yãƙin Tabũka ya kasa jama'ar Musulmi gwargwadon ĩmãninsu da ayyukansu da gabãtarsu a cikin addĩni, cikin darajõji da ɗabaƙõƙi. Darajar farko ita ce, Sahabban farko waɗanda suka tsẽre wa sauran mutãne ga shigã Musulunci da ƙarfin ĩmãni da yawan aiki da tsarkake zũciya ga aikin Allah.
( 2 ) Kungiya ta biyu munãfukai mãsu zurfin wayo, sun san yadda suke ɓõye munãfuncinsu sabõda gõgẽwa da iya munãfunci har mutãne bã zã su iya gãne su ba, sai Allah Ya tõna su.
( 3 ) Wata ƙungiya wadda ta yi munãfunci, tã ƙi fitã zuwa yãƙi amma kuma suka ga sun yi laifi suka yi iƙirãri da cẽwa, « Sun yi laifi, » sa'an nan suka tũba, Allah Ya karɓi tũbarsu.
( 4 ) Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushẽwar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu.