Surah Yunus | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 213
Suratul Yunus from 34 to 42
34. Ka ce: « Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita? » Ka ce: « Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku? »
35. Ka ce: « Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya? » Ka ce: « Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci? »
36. Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
37. Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.
38. Kõ sunã cẽwa, « Yã ƙirƙira shi? » Ka ce:« Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
39. Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance?
40. Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.
41. Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: « Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa. »
42. Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta?
Page No 213 Download and Listen mp3