Hausa translation of the meaning Page No 222

Quran in Hausa Language - Page no 222 222

Suratul Hud from 6 to 12


6. Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta ( 1 ) da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.
7. Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, ( 2 ) dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: « Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa, » haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: « Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne. »
8. Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ( 3 ) ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu.
9. Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci.
10. Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.
11. Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma.
12. Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: « Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi? » ( 4 ) Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.
( 1 ) Matabbatã shĩ ne uba, kuma ma'aza ita ce uwa.
( 2 ) farkon halitta, Al'arshi kõ ruwã. Ruwã da Al'arshi sunã gaba da sammai da ƙasa sa'an nan aka halicci ƙasa daga ruwã kuma aka mayar da ruwa hayãƙi, aka halicci sama . Sa'an nan kuma aka mulmula ƙasa a cikin sũrar ƙwai. Allah neMafi sani.
( 3 ) Me ke tsare ta, watau azãbarme ke hana ta ta zo yanzu?
( 4 ) Sabõda zaman mutãne bã sugirmama mutum sai idan Yanã da wata dũkiya kõ kuma akwai wani ƙarfi bayyananne tãre da shi, to, kai kuma ga zãhiri, bã ka da dukiya kõ wani ƙarfin da zã ka iya tĩlasta su da shi a kan wani abu. Sabõda haka kanã tsõron iyar da duka abin da aka umurce ka, dõmin kada a ƙaryata ka. To, kada ka ji tsõron iyarwã, Allah newakili a kan kõme.