Hausa translation of the meaning Page No 223

Quran in Hausa Language - Page no 223 223

Suratul Hud from 13 to 19


13. Kõ sunã cewa: « Yã ƙirƙira ( 1 ) shi ne. » Ka ce: « Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
14. To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?,
15. Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba.
16. Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta ( dũniya ) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne.
17. Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.
18. Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: « Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai. »
19. Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sunã nẽman ta karkace, kuma sũ ga Lãhira sunã kãfirta.
( 1 ) Kõ kuwa bã zã ka iyar da abin da aka aike ka ba dõmin tsõron su ce: « Kai ne ka ƙirƙira Alƙur'ãni, sa'an nan ka jinginã shi ga Allah. » To, sai ka ce: « Ni mutum ne kamarku, idan nĩ na ƙirƙira Alƙur'ãni, to, bã zai gãgare ku ku ƙirƙira irinsa ba, sai ku zo da surõri gõma irinsa. »