Hausa translation of the meaning Page No 221

Quran in Hausa Language - Page no 221 221

Suratul Yunus from 107 to 5


107. Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
108. Ka ce: « Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba. »
109. Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.
Sũratu Hũd
Tanã karantar da cẽwa Manzannin Allah sun kirãyi mutãnen su zuwa ga tauhĩdi da nau’in kira guda, kuma mutãnen sun fuskãnce su da hãli guda na musu da ƙaryatãwa, sai ka ce a zãmani guda suke, kõ a cikin harshe guda suka yi magana.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki- daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.
2. Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi.
3. Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku.
4. Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne.
5. To, lalle sũ sunã karkatar ( 1 ) da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.
( 1 ) Bã su son su ga mai yi musu wa'azi, sabõda haka idan sun tsinkãyi Annabi daga nẽsa, sai su ɓũya, dõmin kada ya gan su, balle ma har ya yi musu wa'azi. Kuma har idan ya sãme su da wa'azinsa, saisu sanya tufãfinsu su rufe idanunsu da kunnuwansu kamar yadda mutãnen Nũhu suka yi masa a lõkacin da yake yi musu wa'azi. Ka dũba sũratu Nũh' sũra ta 71.