Surah Yusuf | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 240
Suratul Yusuf from 38 to 43
38. « Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa. »
39. « Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam- dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa? »
40. « Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku.Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. »
41. « Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa. »
42. Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, « Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka. » Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
43. Kuma sarki ya ce: « Lalle ne, nã yi mafarki; ( 1 ) nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre- kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa. »
( 1 ) Mafarkin sarki wanda zai zama sanadin fitar Yũsufu daga kurkuku. Wannan yanã nũna ba akẽɓance yin mafarki ga Musulmi kawai, kãfiri ma yanã yin mafarki. Bã a iya fassara mafarki sai da ilmin Alƙur'ãni da Hadisi da kuma sanin al'ãdun mutãne. Mafarki bã ya zama hujja sai idan wani annabi yã fassara shi.