Hausa translation of the meaning Page No 239

Quran in Hausa Language - Page no 239 239

Suratul Yusuf from 31 to 37


31. Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: « Ka fito a kansu. » To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: « Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja! »
32. Ta ce: « To wannan ne fa wanda kuka, zarge ( 1 ) ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu. »
33. Ya ce: « Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai. »
34. Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.
35. Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci.
36. Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ( 2 ) Ɗayansu ya ce: « Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya. » Kuma ɗayan ya ce: « Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa. »
37. Ya ce: « Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa ( 3 ) , kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne. »
( 1 ) A cikin maganar mãtar Azĩz a tsakãnin mãtã bãbu wata kunya, dõmin tã nũna kãsãwarsu. Kuma akwai tsõratarwa ga Yũsufu idan bai yi mata ɗã'a ba ga bukãtarta gare shi.
( 2 ) Yũsufu a cikin kurkuku tare da abõkan shigarsa kurkukun.Kuma yanã fassara mafarki a bãyan kiransa zuwa ga addini.
( 3 ) Kõwane irin abin ne kãfin in gan shi da idõna, zan iya gaya muku nau'insa, kamar yadda Ĩsa ya ce: « Inã bã ku lãbãrin abin da kuke ci a gidãjenku. » A Sũrar Ãl Imrãna ãyã ta 49.