Hausa translation of the meaning Page No 241

Quran in Hausa Language - Page no 241 241

Suratul Yusuf from 44 to 52


44. Suka ce: « Yãye- yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye- yãyen mafarki ba. »
45. Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, « Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni. »
46. « Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani. »
47. Ya ce: « Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, ( 1 ) sai kaɗan daga abin da kuke ci. »
48. « Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa. »
49. « Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha. »
50. Kuma sarkin ya ce: « Ku zo mini da shi. » To, a lõkacin da manzo ya je masa ( Yũsufu ) , ya ce: « Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu. »
51. Ya ce: « Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa? » Suka ce: « Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba. » Mãtar Azĩz ta ce: « Yanzu fagaskiya ( 2 ) ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya. »
52. « Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara. »
( 1 ) Barjn hatsi a cikin zangarniyarsa shĩ ne mãganin ruɓẽwarsa, kõ waɗansu tsũtsõtsi da suke cin sa.
( 2 ) Da wannan magana ta mãtarAzĩza Zalĩha anã fahimtar ita tã musulunta ta hannun Yũsufu kãfin a ɗaure shi.