Hausa translation of the meaning Page No 243

Quran in Hausa Language - Page no 243 243

Suratul Yusuf from 64 to 69


64. Ya ce: « Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama. »
65. Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: « Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki. »
66. Ya ce: « Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku. » To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: « Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa. »
67. Kuma ya ce: « Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam- dabam, ( 1 ) kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara. »
68. Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu,ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
69. Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: « Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa. »
( 1 ) Yãƙũbu ya umurci ɗiyansa su shiga garin, ta ƙõfõfi dabam- dabam, yanã nũna cẽwa yanã gudun kyawunsu da yawansu zai ja hankalin mutãne zuwa gare su. A cikin mutãne akwai mãsu kambun baka da mugun nufi kõ da yake Yãƙũba a cikin hãlin haka ya aza tawakkalinsa ga Allah. Ya yi abin da yake zaton alhẽri ne, wanda bai saɓa wa sharĩ'a ba. Amma kuma yã yi haka ne a kan wani ilmi da Allah Ya sanar da shi cẽwa a wannan fitar tãsu ce Allah zai yi sanadin sãke sãduwarsu da Yũsufu, sabõda haka ya umurce su da su shiga ta ƙõfõfi dabam- dabam, dõmin mutum shi kaɗai yã fi sãmun dãmar ta' ammalin ganin mutãne da abũbuwa. Kuma ta yin haka, yanã tsammãnin waninsu zai ga Yũsufu.