Hausa translation of the meaning Page No 244

Quran in Hausa Language - Page no 244 244

Suratul Yusuf from 70 to 78


70. Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa, « Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne. »
71. Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: « Mẽne ne kuke nẽma? »
72. Suka ce: « Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi. »
73. Suka ce: « Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba. »
74. Suka ce: « To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata? »
75. Suka ce: « Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, ( 1 ) kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai. »
76. To, sai ya fãra ( bincike ) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin ( dõkõkin ) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani.
77. Suka ce: « Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa. » Sai Yũsufu ya bõye ( 2 ) ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: « Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa. »
78. Suka ce: « Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa.Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa. »
( 1 ) Shariar Banĩ yã' aƙũbu ita ce anã bautar da ɓarãwõ shẽkara guda. Wannan shĩ ne shari'ar da Tũrãwa suka ɗauka suka mayar da ita ɗaurin kurkuku da bautar da ɓarãwo a cikin mudda ayyananna.
( 2 ) 'Yan'uwan Yũsfu sun faɗi cẽwa ɗan'uwan Binyaminu ya taɓa yin sãta, dõminsu nũna cẽwa a wajen ubansu tsarkakakku ne daga yin sãta. Shi kuma wanda ya yi sãtan ya gade ta ne daga wajen uwarsa, dõmin wani shaƙĩƙinsa ( Yũsufu ) ya taɓa yin sãta. To, sai Yũsufu ya ce a ransa: « Kũ ne dai mafi sharrin mutãne, Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffintãwa. » Asalinwannan magana wata goggonsa ce ( Shi Yũsufu ) ɗiyar Is'hãƙa, ta riƙe shi, yanã yaro, har a lõkacin da ubansa ( Yãƙũbu ) ya so ya karɓe shi daga gare ta, sai ta yi kaidin sanya kãyan sãta a cikin rigarsa ( Yũsufu ) dõmin ta hana uban ɗaukarsa. A wata ruwaya kuma an ce shi ( Yũsufu ) ya ɗauke wani mutummutumi ne na zĩnãri ( gunki ) ya karairaya shi. Don haka'yan'uwansa suke jingina sãta a gare shi.