Hausa translation of the meaning Page No 246

Quran in Hausa Language - Page no 246 246

Suratul Yusuf from 87 to 95


87. « Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu ( 1 ) da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai. »
88. Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: « Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. ( 2 ) »
89. Ya ce: « Shin, kan ( 3 ) san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai? »
90. Saka ce: « Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu? » Ya ce: « Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa. »
91. Suka ce: « Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure. »
92. Ya ce: « Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama. »
93. « Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya. »
94. Kuma, a lõkacin da ãyari ( 4 ) ya bar ( Masar ) ubansa ya ce: « Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba. »
95. Suka ce: « Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa. »
( 1 ) Anan Yãƙũbu yã bayyana irin ilmi da Allah Ya sanar da shi, cẽwa Yũsufu yanã nan da ransa, kuma sun yi kusa su sãdu da jũna.
( 2 ) Wannan ya nũna ba a haramta sadaka ba ga Annabãwan da suka gabãta, sai ga Annabinmu Mahammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, shĩ da danginsa na kusa aka hana wa cin sadaka.
( 3 ) Yũsufu ya bayyana ga 'yan'uwansa, kuma sun yãfe wa jũna laifi.
( 4 ) Yãƙũba da jĩkõkinsa. Yanã gaya musu, cẽwa yanã shãƙar ƙanshin Yũsufu, su kuma suna jingina shi ga ruɗẽwar tsũfa dõmin rabonsa da Yũsufu shẽkara talãtin da biyar zuwa arba'in.