Hausa translation of the meaning Page No 247

Quran in Hausa Language - Page no 247 247

Suratul Yusuf from 96 to 103


96. Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: « Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah? »
97. Suka ce: « Yã ubanmu! ( 1 ) ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure. »
98. Ya ce: « Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. »
99. Sa'an nan a lõkacin ( 2 ) da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: « Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu. »
100. Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada. ( 3 ) Kuma ya ce: « Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ,Shĩ ne Masani, Mai hikima. »
101. « Yã Ubangijina ( 4 ) lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai. »
102. Wannan daga ( 5 ) lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.
103. Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba,kõ da kã yi kwaɗayin haka.
( 1 ) Ɗiyan Yãƙũbu sunã iƙrãri da laifinsu, sunã nẽman Allah Ya gãfarta musu gahã ɗaya. Ubansu yanã jinkirta nẽmamusu gãfara gun Allah har a lõkacin asuba kõ kuwa daren Jumma'a dõmin ya yi rõƙo a lõkacin karɓar addu'a. Wannan yã nũna anã iya nẽman mai albarka kõ wani mutum yayi wa wani mutum addu'a.
( 2 ) Yũsufu ya sãdu da ubansa da uwarsa. A Larabci anã rinjãyar da uba a kan uwa, a ce ubanni biyu, kuma ga Hausa anã rinjayar da wa a kan uba, a ce uwãye biyu.
( 3 ) Sujada idan ta zama da umurnin Allah ne ga kõwa, to, ba ta da laifi duk yadda take, amma idan an yi ta bã inda Allah Ya ajiye ta ba, to, tã zama kãfirci. A Musulunci gaisuwa da dũƙãwar kai haram ce, waɗansu Malamai sun ce idan ba ta kai ga rukũ'i ba, makarũhi ce, amma idan ta kai ga rukũ'i tã zama harãmunga duka mãlamai, wãtau ijmã'in Malamai sun haramta dũƙãwar da ta kai ga rukũ'i.
( 4 ) Yũsufu yanã addu'a a ƙarshen rãyuwarsa, yanã nẽman Allah Ya cika masa da ẽmãni.
( 5 ) Ƙarfafãwa da ƙãrin tambĩhi daga abin da sũrar ta ƙunsa, daga nan har zuwa karshenta.