Surah Ar-Ra'd | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 252
Suratul Al-Ra'd from 19 to 28
19. Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni.
20. Sũ ne waɗanda suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari.
21. Kuma sũ ne waɗanda suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike.
22. Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla,kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau.
23. Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa.
24. « Aminci ( 1 ) ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida. »
25. Kuma waɗanda ( 2 ) suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.
26. Allah ne Yake ( 3 ) shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan.
27. Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, « Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa? » Ka ce: « Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi. »
28. Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. ( 4 ) To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa.
( 1 ) Sallamar malã'iku a kansu idan sun shiga a gare su, it ce su ce musu: « Aminci ya tabbata a gare ku. »
( 2 ) Bayãnin siffõfin waɗanda suka ƙi karɓar kiran Allah. Watau akasin waɗanda aka yi bayaninsu a bãyã.
( 3 ) Ta'aƙĩbi da tambĩhi ne da ƙãrin bayãni ga mai hankali dõmin ya zãbura ga karɓar kiran Allah.
( 4 ) Ambaton Allah, shĩ ne hukunce- hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: « Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce- hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalansa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba maiyin zikiri ba ne. »