Hausa translation of the meaning Page No 253

Quran in Hausa Language - Page no 253 253

Suratul Al-Ra'd from 29 to 34


29. Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma.
30. Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman. ( 1 ) Ka ce: « Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take. »
31. Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi ( dã ba su yi ĩmãni ba ) . Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã ( 2 ) kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.
32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take?
33. Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada ( zai zama kamar wanda ba haka ba ) ? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: « Ku ambaci sũnãyensu. » Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, ( banda a cikin zũciya ) ? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi! « »
34. Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah.
( 1 ) Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi.
( 2 ) Annabi ya sauka kusa da gidãjen Ƙuraishãwa a rãnar bũɗe Makka. Kuma wannan hukunci yanã nan yanã aiki ga mãsu ƙiyayya da addini, kullum masĩfu sunã aukuwa a kansu har rãnar da Musulunci ya rinjãye su.