Hausa translation of the meaning Page No 262

Quran in Hausa Language - Page no 262 262

Suratul Al-Hijr from 1 to 15


Sũratul Ḥijr
Tanã karantar da wa’azi da umurnin wa’azi da haƙuri da jãrumtaka, sabõda Allah Yã yi alkawarin halaka mãsu izgili ga mãsu wa’azi na gaskiya, kuma mãsu gyãra sũ ne tsayuwar al’umma; dukan musun gaskiya izgili ne.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
2. Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi. ( 1 )
3. Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.
4. Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
5. Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
6. Suka ce: « Yã kai wanda aka saukar da Ambato ( Alƙur'ãni ) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne. »
7. « Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya? »
8. Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, ( 2 ) bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
9. Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato ( Alƙur'ãni ) , kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
10. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
11. Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
12. Kamar wancan ne Muke shigar da shi ( 3 ) a cikin zukãtan mãsu laifi.
13. Bã su yin ĩmãni da shi, ( 4 ) kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
14. Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
15. Lalle ne dã sun ce: « Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce. »
( 1 ) Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yakesanyãwa a ganinsa.
( 2 ) Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne.Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya.
( 3 ) Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini.
( 4 ) Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacinda Allah zai halaka su da azãbarsa.