Hausa translation of the meaning Page No 263

Quran in Hausa Language - Page no 263 263

Suratul Al-Hijr from 16 to 31


16. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
17. Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
18. Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
19. Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
20. Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã ( 1 ) da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
21. Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
22. Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
23. Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
24. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
25. Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
26. Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
27. Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar ( 2 ) iskar zafi.
28. Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: « Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja. »
29. « To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa ( 3 ) a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada. »
30. Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
31. Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.
( 1 ) Muka sanya muku abũbuwan rãyuwa a cikinta, kuma Muka mal1aka muku bãyi waɗanda suke bã kũ ne kuke ciyar da su ba, Mũ ne ke ciyar da su game da ku duka. Wãtau aza abũbuwa a kan ma'auni shĩ ne maslaha rashin yarda da tsaron ma'aunin nan shĩ ne izgili.
( 2 ) Halittar Ãdamu daga yumbu kekasasshe, ya fi daraja bisa halittar Shaiɗan daga harshen wuta, dõmin wuta tanã nũni ga sassabcin hankali da rashin natsuwa
( 3 ) Wannan ya nũnã Ãdamu an yi halittarsa ne da lãka da Rũhi daga Allah kamar yadda aka halitta ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sabõda haka halittar Ãdamu ta fi zama abin mãmãki daga halittar Ĩsã, dõmin Ĩsã asali guda kawai ya rasa daga halittar ɗiyan Adam ta al'ãda, amma halittar Ãdamu tã rasa dukan asalan biyu na uwa da na uba. Haka kuma halittar Hawwã'u, matar Ãdamu tã fi ta Ĩsã ban mãmãki dõmin rashin asalin uwa da ta yi inda ɗã yake ɗaukar lõkacin sũrantãwa, ya fi ban mãmãki daga rashin asalin uba.