Hausa translation of the meaning Page No 27

Quran in Hausa Language - Page no 27 27

Suratul Al-Baqarah from 177 to 181


177. Bai zama addini ( 1 ) ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.
178. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi ( 2 ) a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.
179. Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.
180. Kuma an wajabta, ( 3 ) a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.
181. To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
( 1 ) Bayãnin cẽwa Musulunci bã yin salla ɗai ba ne. A'aha! Musulunci tsarẽwar rãyuwane kamar yadda Allah Ya ce a tsare ta.
( 2 ) Bayãnin hukuncin ƙisãsi: Anakashe namiji sabõda ya kashe mace, bã a kashe ɗa da Musulmi saboda kashin bãwa da kãfiri sai idan ya zama kisan gilla ne kõ ƙwãce. Gilla shĩ ne kashe mutum dõmin dũkiyarsa kõ mãtarsa.
( 3 ) Bayãnin hukuncin wasiyya: Sunna ta bayyan cẽwa bãbu wasiyya ga wanda zai yi gãdo, kuma wasiyya bã zã ta shige sulusin dũkiyar tarika ba.