Hausa translation of the meaning Page No 28

Quran in Hausa Language - Page no 28 28

Suratul Al-Baqarah from 182 to 186


182. To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne,Mai jin ƙai.
183. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta ( 1 ) azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,
184. Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai ( ya biya ) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi ( da wahalar ) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.
185. Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.
186. Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. ( 2 ) Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.
( 1 ) Bayãnin hukuncin azumi da darajar watan Ramalãna wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa.
( 2 ) Bayãnin yin addu'a: Anã sonaddu'a a cikin ramalãna, yadda nẽman karɓar addu'a take bãyan imani. Aikin ƙwarai shine gõɗiyar addu'a.