Hausa translation of the meaning Page No 271

Quran in Hausa Language - Page no 271 271

Suratul Al-Nahl from 35 to 42


35. Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: « Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta. » Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
36. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo ( ya ce ) : « Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci Ɗãgũtu. » To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
37. Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka.
38. Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu ( cẽwa ) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne ( Allah ) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
39. Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã.
40. Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, « Ka kasance; sai yanã kasancẽwa. »
41. Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
42. Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.