Surah An-Nahl | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 278
Suratul Al-Nahl from 94 to 102
94. Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma. ( 1 )
95. Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
96. Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
97. Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
98. Sa'an nan idan ka karantã ( 2 ) Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.
99. Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu.
100. Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne.
101. Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: « Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne. » Ã'a, mafi yawansu bã swa sani.
102. Ka ce: « Rũhul Ƙudusi ( 3 ) ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ( dõmin ) shiriya da bushãra ga Musulmi. »
( 1 ) Wanda yake yin rantsuwa daAllah dõmin ya yaudari wani, to, yanã rũsa kansa ne da kansa, kuma Allah Yanã ɗẽbe jãrumci da natsuwa daga zũciyarsa, sa'an nan kuma yanã da wata azãba mai girma a Lãhira idan Allah bai gãfartamasa ba, da tũba kõ da wani sababi. Snin haka ni'ima ne.
( 2 ) An yi saɓãni ga zaman Isti'ãza gabãnin karãtu kõ a bãyansa. Mãlik ya zãɓi a yi 'Isti'ãza' bãyan karãtu, kõ a bãyan an ƙãre yin salla, dõmin kada shaiɗan ya rinjãyi mutum a bãyan ĩmãninsa da salla. Sabõda haka ya karhanta shi acikin salla. Wasu kuma sunã isti'ãzã a gabãnin karãtu kõ a gabãnin salla.
( 3 ) Rũhul Ƙudusi, watau rai mai tsarki, anã nufin Jibrilu, amincin Allah ya tabbata a gare shi.