Hausa translation of the meaning Page No 279

Quran in Hausa Language - Page no 279 279

Suratul Al-Nahl from 103 to 110


103. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin ( cẽwa ) lalle ne sũ, sunã cẽwa, « Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi. » Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ( 1 ) ne, kuma wannan ( Alƙur'ãni ) harshe ne Balãrabe bayyananne.
104. Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
105. Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata.
106. Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, ( 2 ) fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.
107. Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
108. Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu.
109. Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra.
110. Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta ( 3 ) haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
( 1 ) A'ajami ga asali, wanda bã ya iya maganã da Lãrabci ko dã ga asalin jini shi Balãrabe ne. Asalin maganar akwai wani bãwã Barũme Nasarãni, watau mabiyin addinin isã yanã karatun littattafansa kuma yanã zuwa yanã saurãron Annabi, sai maƙiyã suka ce wai shĩ neyake gaya wa Annabi Alƙur'ãni. Dõmin haka Allah ya yi raddin maganarsu da rashin sanin Lãrabcin wannan mutumin. Sũnansa Kainu kõ jabra.
( 2 ) Ridda ita ce kõmãwa ga kãfirci a bãyan shiga Musulunci. Ba a yin hukunci da ridda ga Musulmi, sai idan ya kãfirta da kansa, bãbu wata tĩlastãwa kuma ya nũna ya yarda da kãfircin, kuma yanã farin cikin da shi. To, hukuncinsa kisa ne, dõmin ya zama ɗan tãwaye. Wannan shĩ ne ma'anar cẽwa akwai fushi a kansa daga Allah. Kuma bã a kashe shi sai an nẽme shi da tũba a cikin kwãna uku, bãbu yunwa, bãbu ƙishirwa. Kuma ayi munãzara da shi kõ zai kõmo. Bayan kwãna uku a kashe shi idan ya ƙi tũba.
( 3 ) Bãyan fitina, yanã nufin wanda ya shiga Musulunci sa'an nan fitinar ridda ta sãme shi, kuma Allah Ya sanya shi ya kõma cikin Musulunci, ya yi abin da Musulunci yake nẽma daga gare shi, na ayyukan ƙwarai gwargwadon hãlinsa, to, Allah Yanã gãfarta masa laifuffukansa na ridda, kuma Yanã jin ƙan sa da rahamarSa.