Hausa translation of the meaning Page No 280

Quran in Hausa Language - Page no 280 280

Suratul Al-Nahl from 111 to 118


111. A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai ( sakamakon ) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
112. Kuma Allah Ya buga misãli, ( 1 ) wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
113. Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
114. Sa'an nan ku ci daga ( 2 ) abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
115. Abin sani kawai ( Allah ) Ya haramta ( 3 ) muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
116. Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, « Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne. » Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
117. Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
118. Kuma kan waɗanda suka tũba ( Yãhũdu ) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, ( 4 ) kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
( 1 ) Kamar Makka. Annabi Muhammadu ya jẽ musu sun ƙaryata shi, sai Allah Yã musanya amincinsu da tsõro, kuma wadãtarsu da yunwa. Wannan shĩ ne sakamakon ridda a kõwane lõkaci.
( 2 ) Bãyan bayãni a kan hukuncin ridda sabõda sanyãwar sãshen ni'imõmin Allah ga wasu gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne sãlihai, sa'an nan Ya yi umurni da cin abin da Allah Ya azurta mutum duka amma da sharuɗɗa uku, watau ya zama halas ga shari'a kuma mai dãɗin ci, wani haƙƙi na wanimutum bai rãtaya ba a kansa ga shari'a, kuma a bi shari'a wajen aikatar da shi kamar yadda Allah Ya ce wajen yanka da mai kama da shi, shi ne gõde wa Allah. Sabõda haka banda kamar giya da kãyan wani mutum sai fa a bisa yardarsa.
( 3 ) Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõminwani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu.
( 4 ) Gabãnin wancan sũra, kamar a cikin sũratul An'ãm ãyã ta l46. Sabõda haka bã a biyar da Yahũdu a wajen haramcin abin da Allah Ya haramta musu, su kaɗai sabõda zãluncinsu.