Hausa translation of the meaning Page No 281

Quran in Hausa Language - Page no 281 281

Suratul Al-Nahl from 119 to 128


119. Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki ( 1 ) da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
120. Lalle ne Ibrãhĩm ( 2 ) ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
121. Mai gõdiya ( 3 ) ga ni'imominSa ( Allah ) , Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
122. Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai.
123. Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka ( cẽwa ) , « Ka ( 4 ) bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.' »
124. Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. ( 5 ) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa,Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar Ƙiyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
125. Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima ( 6 ) da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
126. Kuma idan kuka sãka ( 7 ) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.
127. Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci.
128. Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne.
( 1 ) Wanda ya yi wani abu da Allah Ya hana wajen ni'imõmi ko wajen wani abu dabam nasãɓon Allah, to, idan ya tũbãa gabãnin ya kai ga gargara, Allah zai gãfartã masa. Wannan ni'ima ce.
( 2 ) Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm.
( 3 ) An ambaci Ibrãhĩm sabõda ya gõde wa ni'imõnin Allah dõmin Musulmi su yi kõyi da shi wajen gõde wa Allah ga ni'imõmin da Ya yi ishãra zuwa gare su a cikin wannan Sũra da watanta. Gõde wa ni'imawata ni'ima ce.
( 4 ) Yanã cikin ni'ima ga Ibrãhĩm da kammalarta a gare shi a umurci mafĩfĩcin tãlikai Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, da bin aƙĩdar Ibrãhĩm.
( 5 ) Waɗanda suka sãɓa wa jũna a cikin sha'anin Ibrahĩm wanda yake ya kasance yanã girmama Juma'a dõmin ita ce rãnar cikon ni'imõmin Allah a kan bãyinsa. Yahudu suka sãɓã wa Ibrãhĩm suka girmama Asabar dõmin a rãnar nan ne bãbu wani aiki. Wannan ya dõge har a bãyan ɗauke Ĩsa. Nasãra suka jũya dõmin ƙin Yahũdu zuwa ga Lahadi, dõmin su yi daidai da Kaisara, Ƙustantin, mai girmama Lahadi, rãnar bautã wa rãnã. Kafirce wa ni'ima azaba ce.
( 6 ) Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka, Abin da ake cẽwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.
( 7 ) Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõdahaka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nẽman ni'imar Allah ta ƙãra kammala.