Surah Al-Kahf | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 294
Suratul Al-Kahf from 5 to 15
5. Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.
6. To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki.
7. Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ( 1 ) ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
8. Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta ( ya zama ) turɓãya ƙeƙasasshiya ne.
9. Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo ( 2 ) da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?
10. A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: « Ya Ubangijinmu! ( 3 ) Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana ( sãmun ) shiriya daga al'amarinmu. »
11. Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, ( 4 ) a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.
12. Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin.
13. Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya.
14. Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: « Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. ( Idan mun yi haka ) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan. »
15. « Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu ( waɗanda ake bautawar ) ? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah? »
( 1 ) Sabõda haka ƙawar ƙasa, kamar furen itãcenta ne, bã su ruɗin mai hankali ga tsarewar ladabi tãre da Ubangijinsa, da bin sharĩ'ar Littafin da aka saukar wa Annabi kuma ba a sanya masa karkata ba.
( 2 ) Lõkacin da Allah Ya ce: « kadaAnnabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓimaganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nẽman mutun ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna. »
( 3 ) Sun fara da addu'a ta nẽman shiriya daga Allah, Ubangijinsu. Addu'a tun farko ga kõme ladabi ne. Kuma fãrãwa da nũna bautarsu ga Ubangiji, ladabi ne. Hijira da addini 1adabi ne, kuma amincẽwa da sãmun rahamar Allah, ladabi ne ga Allah, sabõda haka Allah ya jiɓinci tsaron kõgon ya zame musu mafi kyawun wurin zama.
( 4 ) Dũka a cikin kunnuwa, shĩ ne sanya musu barci.