Hausa translation of the meaning Page No 30

Quran in Hausa Language - Page no 30 30

Suratul Al-Baqarah from 191 to 196


191. Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre ( Hurumin Makka ) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake.
192. Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
193. Kuma ku yãƙe ( 1 ) su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.
194. Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa.
195. Kuma ku ciyar ( 2 ) a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
196. Kuma ku cika ( 3 ) hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa ( ya yi aski ) sai fansa ( fidiya ) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.
( 1 ) An umurci Musulmi da tsõkana ga kãfiran da suke nũna musu ƙiyayya bayyane, dõmin su hana su yin addininsu da kyau, kamar yadda Allah Ya umurce su, suna fitinar su dawahalõli. Kuma kada ku bar su, su laɓe da wani watan alfarma kõ hurumi, duk yadda hãli ya yi, a yi haka nan, alfarmõmi nã da ƙisãsi.
( 2 ) Bã a iya yãƙi sai da abinci, kuma bã kõwa ke iya zuwa yãƙi ba, kamar yadda yake bã kowa yake da abinci ba. Sabõda haka sai a ciyar da dũkiya, a tãra ta dõmin ɗaukaka kalmar Allah. Rashin bãyar da ita, to, halaka kai ne.
( 3 ) Hukunce- hukuncen hajji a cikin fitina kõ a cikin rashin lãfiya, idan sun auku a bãyan harama, da hukuncin wanda ya ji dãɗi da umra sa'annan ya yi hajji, kõ kuma ya haɗa su a cikin haramaguda, watau ƙirãni, hukuncinsu ɗaya ne.