Hausa translation of the meaning Page No 29

Quran in Hausa Language - Page no 29 29

Suratul Al-Baqarah from 187 to 190


187. An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i ( 1 ) zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.
188. Kada ku ci dukiyõyinku ( 2 ) a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.
189. Kuma suna tambayar ka ( 3 ) daga jirajiran wata. Ka ce: « Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara. »
190. Kuma ku yãƙi waɗanda ( 4 ) suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.
( 1 ) Abũbuwan da aka hana, a cikin azumi, da ranã, an halatta su da dare har zuwa fitar alfijiri wato sĩlĩli fari na hasken sãfiya da sĩlĩli baƙi na duhun dare. Bã a yin jima'i kõ da dare a hãlin itikãfi, kuma bã a yin itikãfi sai a cikin masallãci.
( 2 ) Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗawannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗinhana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya,shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta.
( 3 ) Shiga Musu1unci yarda ne da barin al'ãdu da hukunce- hukuncen jãhiliyya, sabõda hakaake sãmun tambayõyi da yawa daga sãbon Musulmi kãfin ya kammala da canza tsõfaffin al'ãdunsa da sãbabbi. Allah Yã yi tarbiyar Sahabban Annabi a cikin rãyuwar Annabi, bãyan saukar wahayi.
( 4 ) An umurci Musulmi da tsarekansu da yãƙi ga duk wanda ya yãƙe su, a kõ'ina yake. Sai dai an hana su tsõkanar wasu, kuma an hana su su yi yãƙi a cikin Hurumin Makka sai fa idan an fãɗa su dayãƙi a cikinsa.