Surah Al-Kahf | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 302
Suratul Al-Kahf from 75 to 83
75. Ya ce: « Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba? »
76. Ya ce: « Idan na tambaye ( 1 ) ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni. »
77. Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai ( Halliru ) ya tãyar da shi mĩƙe. ( Mũsã ) ya ce: « Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa. »
78. Ya ce: « Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa. »
79. « Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki ( 2 ) a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi ( lãfiyayye ) da ƙwãce. »
80. « Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci. »
81. « Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi. »
82. « Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ( 3 ) ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa. »
83. Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ( 4 ) ka ce: « Zan karanta muku ambato daga gare shi. »
( 1 ) Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cẽwa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cẽwa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Hani ga al- munkar wãjibi nea cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtarda hukuncin da ya fi tsanani.
( 2 ) Watau wani kamfani ne na matalauta, sunã sana'ar ɗaukar kãya a cikin tẽku, sharika watau kamfani ciniki ya halatta da sharuɗɗansa.
( 3 ) Wannan ya nũna cẽwa kirkinuba yanã amfãnin ɗiyansa, haka gari na sabõda sãmun mutãnen kirki a cikinsa, kamar yadda yake ƙasƙanta da ƙasƙancin mazaunansa bisa dalĩlin da farko an kira garin 'alƙarya' sabõda rõwar mazauna, kuma aka kira shi Madĩna sabõda darajar yãran nan biyu da ubansu da taskarsu. Alƙaryaita ce ƙaramin gari watau ƙauye, kuma Madĩna ita ce babban gari.
( 4 ) Zulƙarnaini an ce sarki ne yanã bin shari'ar lbrãhĩm, ga hannunsa ya musulunta sunansa Askandar. Haliru wazirinsane yanã tafiya a gaban yãƙinsa, kuma ɗan innarsa, watau ɗan khãlarsa ne. Shi ne ya gĩna Askandariyya. Sai dai ga maganar akwai warware jũna. Allah Ya sani. Abin da ke a gabãninmu a nan shĩ ne sanin cẽwa Allah Yã bã shi mulki, ya kõ yi shĩ bisa sharĩ'a, ya yi ƙarfi, da ƙarfin Allah.