Hausa translation of the meaning Page No 301

Quran in Hausa Language - Page no 301 301

Suratul Al-Kahf from 62 to 74


62. To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, « Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan. »
63. ( Yãron ) ya ce: « Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan,dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki! »
64. Ya ce: « Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã. » Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya.
65. Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama ( 1 ) daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu.
66. Mũsã ya ce masa, « Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya? »
67. Ya ce: « Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba. »
68. « Kuma yãya zã ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa? »
69. Ya ce: « Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai haƙuri kuma bã zan sãɓa maka ba ga wani umurni. »
70. Ya ce: « To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato ( 2 ) daga gare shi. »
71. Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, « Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa,kã zo da wani babban abu! »
72. Ya ce: « Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba? »
73. Ya ce: « Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna. »
74. Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: « Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma. »
( 1 ) Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cẽwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. llmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tãauku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa.
( 2 ) Watau sai na gaya maka hukuncinsa da kaina, kuma na ambace shi da kaina.