Hausa translation of the meaning Page No 303

Quran in Hausa Language - Page no 303 303

Suratul Al-Kahf from 84 to 97


84. Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya ( zuwa ga murãdinsa ) .
85. Sai ya bi hanya.
86. Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: « Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu. »
87. Ya ce: « Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma. »
88. « Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi ( watau kyauta ) mai kyau, ( 1 ) kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu. »
89. Sa'an nan kuma ya bi hanya.
90. Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne ( waɗanda ) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta.
91. Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa.
92. Sa'an nan kuma ya bi hanya.
93. Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba.
94. Suka ce: « Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu? »
95. Ya ce: « Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu. »
96. « Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe » . ( Suka kai masa ) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu ( ya sanya wutã a cikin ƙarfen ) ya ce: « Ku hũra ( da zugãzugai ) . » Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: « Ku kãwo mini gaci ( narkakke ) in zuba a kansa. »
97. Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba.
( 1 ) Kyauta mai kyau a nan ba Aljanna ba ce, dõmin maganar ta Zulƙarnaini ce idan ya ciƙasa, yanã iya sanya mãsu ĩmãninta a cikin hãli mai kyau. Amma idan an ɗauki maganar, ta Allah ce, a cikin maganar Zulƙarnaini ga kãfiri,to, a nan 'mai kyau' sai ta zama Aljanna ke nan.