Surah Maryam | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 307
Suratul Maryam from 26 to 38
26. « Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. ( 1 ) To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba. »
27. Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: « Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma! »
28. « Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba. »
29. Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: « Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri? »
30. Ya ce: « Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi. » ( 2 )
31. « Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai. »
32. « Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri. »
33. « Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai. »
34. Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
35. Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. ( 3 ) Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, « Kasance. » Sai ya dinga kasan cẽwa.
36. « Kuma lalle Allah ne Ubangijina ( 4 ) kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici. »
37. Sai ƙungiyõyin ( 5 ) suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
38. Mẽne ne ya yi jinsu, ( 6 ) kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.
( 1 ) Jin sanyi ga idãnu shĩ ne farin cikin sabõda sãmun haihuwa. Ga ibãdar Banĩ lsrã'ĩla, mai azumi bã ya yin magana, amma ga Musulunci Allah Ya shãfe wannan hukunci. Mai azumi yanã magana sai dai anã son ya kãma bãkinsa daga maganar da bã ta ibãda ba.
( 2 ) Wannan ita ce maganar da Ĩsa ya yi wa mutãnen uwarsa dõmin ya barrantar da ita daga tuhuma, kuma ya nũna matsayinsa ga Allah da muƙãminsa na Annabci.
( 3 ) Ba ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi ɗã, dõmin bã Ya mutuwa balle Ya yi bukãtar mai gãdo ga tsaron dũkiya. Shi kaɗai ne, bã Ya bukãtar wani ɗã mai tsaron dangi dõmin kada su bar hanya.
( 4 ) Tana a cikin maganar Ĩsã a lõkacin da ya girma yana wa'azi ga mutãnensa, sabõda haka aka raba ta da maganar farko a lõkacin da yake jãrĩri.
( 5 ) Bãyan ɗauke Annabin Allah Ĩsã ɗan Maryama ƙungiyõyin mutãne sun sãɓa wa jũnansu a cikin sha'aninsa. Yahũdu suna sũkar sa, Nasãra suka kasu uku: Nasũriyya suka ce: « Shi ɗan Allah ne » Malakaniyya suka ce: « Shi ne na uku ɗin uku, » Ya'aƙũbiyya suka ce: « Shi ne Allah. » Sabõda haka Nasara sukahaihaye kuma suka zurfafa, sa'an nan Yahũdu suka taƙaita kuma suka yi sũka gare shi.
( 6 ) A rãnar Lãhira a lõkacin daake yi musu hisãbi a gaban Allah ganinsu da jinsu sunã da kyau ƙwarai, amma a nan dũniya sunã a cikin makanta da kurumci sabõda ɓatar da suka yi, suka ƙaryata Ĩsã, aminci ya tabbata a gare shi.