Hausa translation of the meaning Page No 308

Quran in Hausa Language - Page no 308 308

Suratul Maryam from 39 to 51


39. Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
40. Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
41. Kuma ambaci Ibrãhĩm ( 2 ) a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
42. A lõkacin da ya ce wa ubansa, « Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka? »
43. « Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici. »
44. « Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama. »
45. « Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan. »
46. Ya ce: « Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci. »
47. Ya ce: « Aminci ( 3 ) ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni. »
48. « Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina. »
49. To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.
50. Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya ( 4 ) maɗaukaki.
51. Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
( 1 ) ( 1 ) Tun da yake Mũ ke gãdon ƙasa da wanda yake a cikinta,bã zã Mu yi bukãtar sãmun wani magãji ba.
( 2 ) Ibrãhĩm ya yi ƙõƙarin shiryar da ubansa, sai dai Allah bainufi shiryuwarsa ba. Daga cikin amfãnin haihuwa akwai abin haihuwa ya shiryar da mahaifinsa, ya yi masa nasĩha gwargwadon hãli.
( 3 ) Ibrãhĩm yã mayar da magana mai kyau da laushi da aminci ga maganar ubansa mai mũni da gautsi da tsõratarwa. Wannan yanã kõyar da yadda ake kira zuwa ga Allah da kuma yadda ya kamãta a tausasa wa uba kõ dã shi kãfiri ne.
( 4 ) Harshen gaskiya, shi ne yabomai kyau daga Allah da mutãne. Wanda ya yanke wa mutãnenSa dõmin Allah, to, zai sãka masa da waɗansu mutãnen kirki dõmin su ɗẽbe masa kẽwa.