Hausa translation of the meaning Page No 309

Quran in Hausa Language - Page no 309 309

Suratul Maryam from 52 to 64


52. Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
53. Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
54. Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
55. Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens ( 1 ) da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
56. Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
57. Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
58. Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
59. Sai waɗansu 'yan bãya ( 2 ) suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.
60. Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
61. Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa ( mãsu aikin ĩmãni ) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.
62. Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.
63. Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
64. ( Sunã mãsu cẽwa ) « Kuma bã mu sauka ( 3 ) Fãce da umuruin Ubangijinka ( Muhammad ) . Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan. » Kuma ( 4 ) ( Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.
( 1 ) Mãtarsa da 'ya'yansa da Jurhum, yanã umurninsu da salla da zakka. Yanã wajaba ga mutum ya umurci iyalinsa da tsare haƙƙõƙin Allah.
( 2 ) An ruwaito cẽwa wannan zai auku a lõkacin Tãshin Ƙiyãma ne a bãyan tafiyar sãlihan wannan al'umma ta Muhammadu. Zã su dinga barbarar jũnansu a cikin hanyõyi. Su tõzarta salla, su gina manyan gidãje su hau dukan abin da aka hana su, su tufanci abin da aka hana su, Ƙurɗabi.
( 3 ) 'Yan Aljanna sunã cẽwa ba mu sauka a waɗannan gidãje ba sai da umurnin Ubangijinka, kai mai karatu, A1lahne Mai mallakar kõme, kuma kõme ãyã ne mai nũni zuwa gare shi, sabõda haka bã a mantãwa da shi.
( 4 ) Maganar Allah ce a bãyanmaganar 'yan Aljanna dõmin ta'aƙĩbi da ƙãrin bayãni ga maganarsu.